29 Agusta 2025 - 18:19
Source: ABNA24
Mayakin Gwagwarmayar Hizbullah Ya Yi Shahada A Harin Da Isra'ila Ta Kai A Kudancin Lebanon + Bidiyo

Wani dan gwagwarmayar Hizbullah ya yi shahada a wani hari da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai a garin "Sir al-Gharbiyah" kudancin Lebanon + bidiyo

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbay (As) – ABNA – ya habarta cewa: wani dan gwagwarmayar Hizbullah na kasar Labanon ya yi shahada a wani hari da wani jirgin yakin haramtacciyar kasar Isra'ila ya kai kan wata mota a garin "Sir al-Gharbiyah" da ke kudancin kasar Lebanon.

An kai harin ne a kusa da kofar gabashin garin a kusa tashar Al-Salam inda shahadar shahid "Ahmad Naeem Ma'touk" ta auku.

A cewar rahotannin yankin, Ahmad Ma’touk ya samu rauni a baya sakamakon fashewar wani na’urorin Faigar da ta faru. Wani harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai masa ne a cikin motarsa ​​ta kashin kansa a lokacin da yake komawa gida daga ofishin likitan ido.

Lamarin dai ya faru ne yayin da rikicin kan iyaka a kudancin kasar Labanon ke ci gaba da ruruwa sannan kuma hare-haren da Isra'ila ke kai wa a sassa daban-daban na kasar ya tsananta a 'yan kwanakin nan.

...................................

Your Comment

You are replying to: .
captcha